AYYUKAN YAU DA KULLUM NA MINTI BIYAR
Hade-Hade Masu Kyau

Ya kamata mu daina zubar da shararmu a cikin magudanun ruwa. Nan ba da ɗadewa ba kogunanmu za su cike da tarkacen robobi fiye da kifaye. In haka ta faru me za mu ci?
Akan sami tsuntsaye da dabbobi suna mutuwa a sakamakon robobi da suka cika musu tumbi. Ayu babban kifi ne, ka kuma yi tunanin irin yawan sharar da suke haɗiya.

Hakkin mallaka Polly Alakija
Hakkin mallaka SCOTTISH MARINE ANIMAL STRANDINGS SCHEME

Wannan kifin ayun yana ɗauke da tarkace roba mai nauyin kilogiram 100 a tumbinsa.

Kana buƙatar guntayen takardu huɗu, masu girma daidai wa daida.

Ka zana layi a tsakiyar bayan kowace takarda.

Ka sanya maki masu tsawon santimita bibbiyu da kuma santimita hurhɗu a bayan wannan layi da ke kan kowace takarda.

Ka rubuta wasu haruffa guda huɗu. A jera su daidai da makin nan da aka yi a bayan takardar.

Me ke cikin tumbinsu? Tumbin ya yi daidai da makin da ke tsakiya.

Hakkin mallaka Polly Alakija

Ka yanka hotunan a daidai tsakiyar layin.

Ka hautsina haruffan domin ka samar da wasu sabbin alamomin hoto!