AYYUKAN YAU DA KULLUM NA MINTI BIYAR
Zanen kaina
Yanzu bari na zana hoton kaina. Kana buƙatar madubi domin ka kalli kanka sosai. Ka fara da koyon zana siffar ƙwai.

ka zana babbar siffar ƙwai na kanka.

Idanuwanka suna daga tsakiyar kanka, sannan ƙasan hancinka yana tsakanin idanuwanka da haɓarka. Ka gane? Da kyau! To, ya rage naka.
Zanen kai yana nuna mana abin da kake tunani game da kanka.

“Tsarabar Aure” ta Njideka Akunyili Crosby.

“Ba Makarnta Yau” na Yinka Quinn