BA NI LABARINKA
Ka Ƙirƙiro Labarai

Akwai abubuwa da dama da za ka iya yi da murafen kwalba. Maza, ka fara tara su!

Ka tara murafen kwalba da DAMA. Ka yi amfani da fenti ko jan-farce ka zana haruffa a kan murafan kwalbar nan. Idan ka tara haruffan da dama, sai kuma ka ci gaba da wasan.

Kana buƙatar:

  • Murafen kwalbar da aka rubuta harufan
  • Aboki

Ku riƙa yi juyi-juyi, kuna sarrafa kalmomi daga murafan kwalbar nan. Ku tsara wasan ta hanyar bayar da adadin lokaci!

Hakkin mallaka Ijeoma Okoye
Hakkin mallaka Polly Alakija

Wane irin wasa kuma za ka iya yi da murafen kwalbar?