BA NI LABARINKA
ka naɗe shi ciki ka kuma naɗe shi waje

Ka juya bayan takardar taka ta kalli sama, sai ka naɗe daga dungu zuwa dungu. Sai ka ware ta.

Za ka ga babbar alamar X ta ratsa tsakiyar takardar taka.

Ka naɗe kowace kusurwa zuwa tsakiyar murabba.

murabbarka za ta kankance.

Ka juya murabbar.

Ka naɗe kowane dungu zuwa tsakiyar murabbar.

murabbarka za ta sake ƙanƙancewa.

Ka naɗe sannan ka ware sikwayar taka zuwa rabi-rabi a kowane bangare.

Ka juya murabbar.

Ka cusa yatsarka ƙasan fuka-fukan, ka turo kusurwowin waje zuwa tsakiya.

Yadda za a yi wasan:

1. Kana rike da Madaukin Labarinka, ka tambayi abokinka ya zabi wani hoto da ke wajen Madaukin Labarin. Ka fadi kalmomin hoton da ka zaba, sannan ka buɗe ka kuma rufe Madaukin Labarin tare da harafin da ke kan kowace kalma. Wannan shi ne mafarin labarin.

2. Ka tambayi abokin naka ya zaɓi lambobi biyu da ya gani a ciki. A tara waɗannan lambobin wuri ɗaya. A buɗe, a kuma rufe maɗaukin labarin na adadin waɗannan lambobin. Labarinka dole ya ƙunshi wannan lambar.

3. Abokin naka zai sake zaɓar wata lambar.

4. A buɗe murfin maɗaukin labarin a ƙasan wannan lambar don a ga surar da ke ciki.

MU JE ZUWA!!

Zazzage kuma Yi!

FCI Five Cowries Online My Story of Water 'Download and Do' Icon
Hakkin mallaka Polly Alakija

Za ka sauke ka kuma buga mafaɗin labarinka a nan, ko kuma ka tsara naka!