GA MAI FASAHAR ZANE-ZANE
Agostino Moreira de Melo

Hakkin mallaka Polly Alakija

Agostino Moreira de Melo ɗan ƙasar Brazil ne.

Yana amfani da tsofaffin kayayyaki domin ya ƙirƙiri wasu kyawawan abubuwa.

Hakkin mallaka Agostino Moreira de Melo
Hakkin mallaka David Earle

Waɗannan sun yi kama da kan mazari, amma an yi su da murfin kwalabe ne da kuma murafen roba. Ko ka taɓa sarrafa irin waɗannan? Dole ka mayar da hankali in ba haka ba abin ba zai yiwu ba!

Agnostino yana sha’awar kare muhalli. Yana amfani da fasaharsa domin ya jawo hankalinmu mu san mu su waye. 

Hakkin mallaka Rebeca Mojica jewelry
Hakkin mallaka Agostino Moreira de Melo

“Surar Mandala”

Surar alama ce da jama’a da dama a duniya suke amfani da ita domin samun natsuwa. Surar Mandala galibi da’ira ce. Dukkan surorin Mandala suna da manufa guda.

Ka ƙaddara abin da zai faru idan abu ya faɗa cikin ruwa kuma ka kalli yadda igiyar ruwa take watsuwa a kan ruwan.

Agostino yakan so mu kalli abu ta fuskoki daban-daban, kuma mu tambayi kanmu ko mun kasance yadda muke so mu kasance?

Hakkin mallaka Agostino Moreira de Melo
Hakkin mallaka Agostino Moreira de Melo