GA ‘YAR GWAGWARMAYA
Amariyanna Copeny

Hakkin mallaka LuLu Brezzell

Tun Amariyanna tana ‘yar shekara 8 ta fara kamfen domin kare ruwan garinsu.

KAI MA KA ZAMA ƊAN GWAGWARMAYA!

Ya rage naka wajen ƙoƙarin kawo sauyi! Ka yi tsayin daka na ganin cewa mutane ba sa zuba shara cikin rijiyoyi da koguna da rafuka ko magudanun ruwa domin hakan yana gurɓata muku ruwan sha kuma yakan jawo cuta.

An haifi Amariyanna Copeny a shekarar 2007. Ita ‘yar garin Flint ne na ƙasar Amurka. Ruwan garin su Amariyanna duk ya gurɓace. Kan haka ta rubuta wa Shugaba Obama tana tambayarsa ya yi maganin wannan matsalar, kuma ya yi!

Hakkin mallaka PURPOSE/FOOTAGE FILMS
Hakkin mallaka Jake May

Ka duba madubi.

Wa kake gani?

Ko za ka iya zama ɗan gwagwarmaya?

Wane sauyi kake fatar kawowa ga al’ummarka?

Ta yaya za ka iya jawo hankalin mutane su saurare ka? Za ka ɗinka ‘yan riguna ne, ko huluna ko ka rubuta wa Shugaban ƙasa? Kai ma za ka iya fa!

Hakkin mallaka LuLu Brezzell

Ka Sauke Ku Kuma Juya Shi Zuwa!

FCI Five Cowries Online My Story of Water 'Download and Do' Icon
Hakkin mallaka Polly Alakija

Mene ne saƙonka? Ka yi shi cikin sauƙi!