KA AJIYE KOMAI KA YI ZANE
Bari mu Zana Tsuntsaye
Ga wasu tsuntsaye daga Fasahar zane ta Afirka.

Sassaƙaƙƙen tsuntsu na katako daga ƙasar Guinea.

Jeren tsakiya mai siffar hankaka daga Afirka ta Kudu.

Zakaran azurfar Benin daga ƙasar Nijeriya.
Dubi waɗannan kyawawan tsuntsayen Afirkan da suke zaune a bakin ruwa ko kusa da shi. Dukkan waɗannan tsuntsayen suna fuskantar barazanar ƙarewa saboda abincinsu da muhallinsu duk suna fuskantar barazana saboda gurɓata.

Maikin ruwa

Zalbe

Agwagwar ruwa
Dubi dabbobi da tsuntsaye da ke kewayenka. Abubuwa da dama an yi su da siffar ƙwai da kuma da’ira. Idan za ka iya zana da’ira da kuma siffar ƙwai to za ka iya zana tsuntsu! Da koyo akan iya! Ka koyi yadda ake zana sauƙaƙan surori da farko.

Ka fara koyon zana lanƙwashe-lanƙwashe.

Ka koyi zana da’irori masu siffa daban-daban da kuma siffa iri guda.

Yanzu sai ka fara da siffar ƙwai da siffar sarƙa.

Ka yi ƙoƙarin zana fuka-fukai da gasu.

Ka zana sauƙaƙan surori na tsuntsaye a yanayi mabambanta.
Yanzu ka gane makamar zancen!



Copyright Polly Alakija