KA AJIYE KAMAI KA YI ZANE
Mafarkin Kamu

In kai masunci ne, me kake fatar kamawa a Mafarkin Kamunka?

Bari mu fara koyon zana da’irori da kamfas. Kuma yanzu komar kamun kifi za mu zana.

Ba matsala idan ma ba ka da kamfas; za ka iya yi da takarda.

Da koyo akan iya! Ka zana tsayayyun da’irori da kamfas ɗin naka.

Ka ƙara wasu layuka wanda shi zai ba ka komar kamun kifi!

Mene ne ba ka so a cikin komarka?

Me kake so a cikin komarka?

Yanzu sai ka fara ƙirƙirar!

Yaya Mafarkin Kamunka zai kasance?

Hakkin mallaka Polly Alakija

Ni ga yadda nawa yake!