KAI MA ZA KA IYA
Babban Kamu
In kai masunci ne me kake son gani a cikin komarka? Ka yi tunanin yadda yadda take kasancewa a ruwa. Me za ka gani? Kifi ko tarkacen roba ko kuma Aljanar ruwa? Yanzu bari mu yi surar abin adana halittun ruwa domin mu ga abin da kake tunani yake a cikin ruwa.

Kana buƙatar:
- Tsohon akwatin kwali
- Takarda
- Gam na ruwa
- Almakashi
A ƙawata cikin wannan kwali da wasu ƙyallaye. Sai ka fente shi daga ciki.

1. Ka zana wasu surori da kake tsammani za ka iya gani a ƙarƙashin ruwa. Idan ka yi amfani da kakkaura ko siririn alƙalami ko fensir to zanen naka zai yi kama da na wani ƙwararre. Ka yi amfani da kakkauran alƙalami wajen zana manyan alamomi, sannan ƙarami domin sauran bayanai.

2. Ka zane surorin don ka fitar da kowace siffa.

3. Ka zurara “kamunka” cikin abin adana halittun ruwan.
