KAI MA ZA KA IYA
Daga Shara zuwa Kyawawan Furanni

Dubi waɗannan kyawawan furanni da ƙwararriyar mai zanen fasahar nan ‘yar ƙasar Czechoslovakia, Veronica Richerterová, ta samar. Ko ka gane da me ta samar da waɗannan furanni?

Hakkin mallaka Veronica Richerterová.
Hakkin mallaka Veronica Richerterová.
Hakkin mallaka Veronica Richerterová.

Kai ma zaka iya!

Abubuwan da kake buƙata kawai su ne:

Kwalaben roba

Igiya

Almakashi

Za ka yi wa kwalaben fenti tun kafin ka fara, amma ka tabbata ka yi amfani da fentin ruwa.

Umurni:

1. Ka yanke ƙasan kwalaben naka.

2. Ka yanka kwalbar daga ƙasa zuwa sama domin ta yi kama da reshen fure. Za ka yi hakan don ka samar da dogaye da gajeru da sirara da kuma masu faɗi. Sai ka lallanƙwasa su ka kuma murɗa su.

3. Ka ɗaure su wuri guda, sai ka rataye. Yana da sauƙi! Za ka iya da ƙara manna ganyaye a jikin igiyar.

Hakkin mallaka Polly Alakija
Hakkin mallaka Richard Adefusi