KAI MA ZA KA IYA!
Dangar Kifi

Mai fasahar zane Nnena Okore takan saƙa siffofin abubuwa daga ababe da dama.

Hakkin mallaka Nnenna Okore

“Danga” ana yin ta ne da itatuwa da kuma tsoffin jaridu. KAI MA ZA KA IYA WANNAN!

Kana buƙatar itatuwa da jakakkunan leda da fallen jaridu da kuma igiya. Ka yanka jakakkunan ledar da takardar zuwa kamar sili-sili, ka miƙar da su kamar igiyoyi.

Mu je zuwa!

Hakkin mallaka Polly Alakija