KAI MA ZA KA IYA
Kyakkyawan Kifi

Masassaƙa na Jamhuriyar Benin ne suka yi waɗannan kyawawan kifin. Sun yi su ne da abebaɗen da ake iya sabuntawa.

Kai ma za ka iya!

Abin da kake buƙata su ne:

  • Jakakkunan leda
  • Tsohuwar takarda
  • Tsohon kati
  • Almakashi
  • Gam na ruwa

1. Ka yanka jakakkunan robar sili-sili ka kuma ɗaɗɗaure su kamar igiya.

2. Kana buƙatar tsoffin kwali domin ka suranta kifi.

3. Ka kalmashe takardar zuwa rabi.

4. Ka zana siffar rabin kifi a kan kalmasa guda.

5. Ka fara yanka!

6. Ka buɗe ka ga kyakkyawan kifinka!

7. Ka siffanta katin zuwa siffar kifi don ya yi daidai da kifinka na takardar.

8. Yanzu sai ka sanya idanduna!

Hakkin mallaka Polly Alakija

9. Ka ɗaure kyakkyawan kifinka a kan igiyarka.

Yaya kyakkyawan kifinka yake?