ME YAKE FARUWA A NAN


Hakkin mallaka Polly Alakija
Yara daga kwalejin Badore, Legas, Nijeriya tare da zanen kwalekwalensu mai suna “Ciki ya Cika”.
Ka taɓa jin karin maganar da ke cewa “Kamannunka abincinka”? Haka kuma yadda kake ya danganta da abin da kake sha. Domin ka kasance cikin lafiya da kuzari a kullum kana buƙatar shan ruwa kimanin lita ɗaya da rabi (1.5), ko ma fiye da haka a lokacin rani.

Shin rowan shanka tsaftatacce ne? Wannan rowan famfo ne da aka gani tare da taimakon na’urar girmama abu.
Daga ina kake samun rowan shan ka? Za a iyaganin sa garau amma kila yana ɗauke da ƙananan ƙwari waɗanda ido ba ya iya gani, in ka sha kuma ya sanya maka ciwo. Ka tabbata duk ruwan da za ka sha sai ka tafasa shi na tsawon aƙalla minti guda domin hakan zai kashe dukkan ƙwayoyin cutar da ke ruwan.

Shin wannan rowan kuwa tsaftatacce ne? za ka iya cin kifin da aka kama a nan?
Idan ruwanka ya gurɓata da wata guba tafasa ruwan kawai ba zai tsaftace shi ba. Don haka sai ka kiyaye inda za ka nemo rowan shanka. Idan kana ɗebo ruwa daga juji ne ko inda manoma suke fesa maganin ƙwari, to rowan yana ɗauke da sinadarai masu guba da za su iya cutar da kai.

Ko ka san abin da ya kasha wannan ayu ɗin?
Idan ruwa ya gurɓata zai iya shafar rayuwar kifin da ke ciki ya kuma sanya masa cuta domin sukan ci daga abin da ya gurɓata. Ɗan’adam kan jefa tarkacen da aka yi da roba cikin magudanan ruwanmu wanda hakan zai kasance nan da shekaru 30 masu zuwa zai kasance muna da waɗannan tarkacen robobin a koguna da tekunanmu fiye da adadin kifayen da ke ciki. Saboda haka mece ce makomar iyalan da suka dogara da kamun kifi don tafiyar da rayuwarsu?



A Nijeria muna da nau’o’in tsuntsu mayen kifi guda 10. Waɗannan kyawawan tsuntsaye suna cin kifi ne, don haka ne ma Allah Ya yi su da dogon baki. Idan ruwan ya cika da tarkacen robobi me za su ci? Dabbobi da tsuntsaye a kullum sai mutuwa suke yi a faɗin duniya saboda cikinsu ya cika da tarkacen robobi da suka ci. Ya rage naka! Domin ka kawo sauyi ka kare mu.






Copyright Polly Alakija