MU JE GA SANYA LAUNI
Twin Seven Seven

Twins Seven Seven, 1944-2011, ya kasance a garin Ibadan ne ta Nijeriya. Yana sha’awar zanen fenti da waƙa da kuma rawa.

Hakkin mallaka Twin Seven Seven

“Maharbi da Raƙumin dawa”

Waye kake gani yake da ƙarfin iko a nan?

Hakkin mallaka Twin Seven Seven

“Masunta Masu Albarka”

Me kake tsammani waɗannan masunta za su kama in da a yau suke kamun kifin?

Hakkin mallaka Twin Seven Seven

“Ragwayen Mafarauta da ‘Yan Kokawa Masu Dafi: Ƙadangare da Fatalwoyi da kuma Kumurci”.

Waye zai ci wani?

Twins Seven Seven yakan bayar da labarai ne a cikin hotunansa da suka danganci al’adun Yarbawa. Hotunansa da dama suna bayar da labarai kan yadda mutane da dabbobi suke dogara da juna.  Za ka iya sanya launi a kan naka hoton Twins Seven Seven ɗin. Za ka iya ƙara naka alamomin.

KA SAUKE KA KUMA Yi!

FCI Five Cowries Online My Story of Water 'Download and Do' Icon

Hakkin mallaka Polly Alakija