SHIRI DOMIN NUNI
Kwalba da Ciki da kuma ‘Yan Kwikwiyo

Ƙera waɗannan ‘yan kwikwiyon yana da sauƙi SOSAI!

Hakkin mallaka Polly Alakija

Abubuwan da kawai ake buƙata su ne kwalaben roba da almakashi da itatuwa da kuma tunanin labarin da za a tsara! Za ka iya amfani da kalmomi daga cikin “Ciki cike da tunani” a tsarin labarin naka.

1. Ka juya kwalaben naka kansu yana duban ƙasa.

2. A sanya ice a ciki.

3. A yi fenti ko zanen fuska a jikin kwalbar, sai a gusa can gefe. Za a iya sanya gashi ko hula waɗanda su ma za a iya yi musu fenti. A tabbata an yi amfani da fentin ruwa.

Hakkin mallaka Wasiu Quadri