KAYAN AIKI
Yaya?

Masanin kimiyya na Ankara!

Duk muna ƙaunar ANKARA. Muna ƙaunar alamomi masu maimaita kansu da a wani lokaci suke ba mu wani labari.

Me ka gani a cikin waɗannan alamomi?

Wasu daga cikin sharar nan suna yawo a kan ruwa, wasu kuma sukan nutse ne.

Bari mu ga abin da yake faruwa da magudanun ruwanmu idan muka watsa shara a makwarari da ƙoramu da kuma koguna.

Kana buƙatar:

Tarkacen kwalaben roba

Ruwa

Wasu abubuwa: mai da ƙasa da shinkafa da wake da guntayen abebaɗe na roba da sauransu.

1. Ka cika kwalabenka da ruwa.

2. A zuba abubuwa mabambanta a cikin kwalaben. A jijjiga kwalbar!

3. Me yake yawo a saman ruwan? Me kuma ya nutse ƙasa? Me yake yawo a tsakanin ruwa?

4. Ka zana surar sakamakon da ka gani.

5. Ka sake maimaita yadda ka samu wannan sakamakon gwajin.

6. Ka zana wasu alamomi daga bayan zanen.

7. Ka sanya launi da cewa: Kai masanin kimiyya ne na Ankara!