ƊAKIN ADANA KAYAN ZANE-ZANE

Shekaru da dama ana amfani da dabbobi a fannin fasaha wajen isar da saƙo. Idan mutum ya ajiye hoton zaki ko karankanda a gidansa, me hakan yake nufi? IIdan mutum yana da hoton ɓera ko tsutsa me wannan yake nuni a game da su?

Dabbobi da dama suna fuskantar barazana a wannan ƙarni na 21. Masu zanen fasaha suna alamta su da matsayin kare muhalli.

Copyright Benin Art

Waɗannan damisoshin na tagulla guda biyu tun na ƙarni na 16 ne daga Benin ta Nijeriya. Damisoshi na tagulla irin waɗannan ana amfani da su ne kamar masu gadi a ƙofar fadar Oba.

Copyright Jose Rodriguez

Tsakiyar gargajiya ta Yarbawa a ƙarni na 20. Tsakiyoyin gilashi suna da daraja. Me kake zaton hoton giwa da na mikiya suke wakilta?

Copright falko1 Graffiti

Fentin jikin bango na CALDER daga birnin Cape Town, na ƙasar Afirka ta Kudu. Ko da ƙaramin gida zai iya kasancewa zane na manyan dabbobi!

Copyright William Kentridge, South Africa 2019

Zanen “Karakanda” na William Kentridge, ɗan ƙasar Afirka ta Kudu a 2019. Karakanda dabbar daji ce, mafaɗaciya. Me ya sa kake gani mai zanen ya zana daron abinci a bakinta?

Copyright Cai Guo-Qiang

“Gado” na Cai Guo-Qiang, ɗan ƙasar Australia, a 2013. Dabbobi da mutane duk suna buƙatar samun tsaftataccen ruwa.

Copyright Polly Alakija

Fentin jarkoki na “Ciki ya cika” da aka yi a 2019, a Ijebu ta Nijeriya.

Wace dabba za ka zaɓa domin ta wakilci yadda kake? Yaya za ka nuna wannan dabbar? Ka shirya yin zane da fenti da kuma sassaƙa? To, mu je zuwa!