ƊAN AIKI NA MINTI BIYAR
Fuskance Ni In Fuskance Ka

Wani lokaci mukan fuskanci juna saboda muna son juna.

Copyright Polly Alakija

Wani lokaci mukan fuskanci juna saboda babu wata dama ta mu fuskanci wani wurin na daban!

Copyright Modimolle, South Africa; Jan 2011
Copyright Konrad Lorenz
Copyright Hudson Bay Manitoba Canada

Yanzu mu taɓa ɗan aiki!

Kana buƙatar fensiri guda biyu: ɗaya ga kowane hannu, sai kuma ‘yar takarda.

Ka bai wa kanka lokaci.
Ka bai wa kanka minti biyar.
Duk hannayen naka za su yi rubutu a lokaci guda.
Ka zana surar fuska. Za ta iya kasancewa taka, ko ta babban abokinka, ko kuma ta wata dabba.

Copyright Polly Alakija

Shin fuskokin naku suna fuskantar juna saboda kuna son juna, ko kuma saboda ba ka da wani zaɓi?!