FAGEN WAƘA
Kaɗan mai Yawa
Wani lokaci za ka iya yin tasiri sosai ta hanyar magana ‘yar kaɗan. Wani lokaci mawaƙi Chuma Nwokolo yana amfani da kalmomi kaɗan ne.
ƘAREWA
A kan Tsibirin Faroe
A nan Ƙauyen Muli yake
Inda babu kowa.
na Chuma Nwokolo
Tsibirin Faroe yana can gefen gaɓar Scotland.

Idan da a ce akwai milyoyin mutane a kan Tsibirin Faroe to da yaya waƙar za ta kasance?
Ko za ka iya rubuta waƙa a kan ƙarewa?
A da can Tsibirin Legas mazaunin dorina da kadoji ne. Amma a yanzu cike yake da gine-gine da kasuwanni.
ƘAREWA
A Legas
Akwai wani Tsibiri
Da babu dorinar ruwa.
na Olumide
Yanzu damar taka ce!
