GA WANNAN MAI FASAHAR ZANEN
Sunansa Dyalan Lewis

Ga Dyalan nan yana aiki a ɗakin zane-zanensa
Dyalan Lewis mai sassaƙe-sassaƙe ne daga ƙasar Afirka ta Kudu. Yana son dabbobi.


Dyalan Lewis yana amfani da fasahar zanensa wajen faɗakar da mutane buƙatar kare muhalli da kuma dabbobi. Abin da ya zaburantar da shi da farko, ita ce damisa wadda a da ake ganin ta tana yawatawa a dazukan nahiyar Afirka, amma yanzu kusan ta ɓace.


A da, Dyalan Lewis yana suranta abin ne da laka, daga bisani kuma sai ya yi zubi a ruwan tagulla. Ita tagulla haɗe-haɗe ce na ƙarfe da tama da kuma kuza. Wannan tsohuwar hanya ce. Masu fasahar sassaƙa a Nijeriya suna zubi da tagulla tun shekaru dubbai da suka wuce.



Wannan damisar azurfar an samo ta ne daga Benin.