GA WANNAN 'YAR GWAGWARMAYAR
Vanessa Natake

Ga Vanessa.
An haifi Vanessa a ƙasar Uganda a 1996. Ta damu da yadda duniya take ƙara ɗumama da kuma ƙarancin ruwan sama a ƙasarta. Daga nan ta zama ‘yar gwagwarmaya. Ita ce ta farko ‘yar gwagwarmaya da ke wajen mashigar Majalisar ƙasar Uganda. Amma daga baya yunƙurin nata ya jawo hankalin wasu matasa da suka kira kan su da suna “Samari na Afirka ta Gobe”.


An lalata dazuzzukan ƙasar Congo. Me za ka iya yi domin ka kare makomar wannan duniyar?
Ƙungiyar Samari na Afirka ta Gobe suna shelar kare dazuzzukan Congo. Ba wai sai manya ne kawai za su iya kawo sauyi ba. Kai ma za ka iya kawo sauyi! A yanzu haka Vanessa tana magana da shugabannin duniya ne.


Me kake fatar sauyawa? Ko za ka iya zana wani samfoti da yake ɗauke da wannan saƙo da yake gaya wa jama’ar duniya da ba ka iya harshensu ba?
Ka sauke ka kuma Aikata!