KA AJIYE KOMAI KA YI ZANE
Dorina cikin Farin Ciki da kuma Wasu Siffofi masu Surar Ƙwai

Akwai wasu nau’in dorina a Nijeriya, sai dai ba su da yawa. Dorina tana cikin dabbobin da ke barci da rana, su kuma farka da dare. Me ya sa kake gani suke yin hakan?

Copyright The Metropolitan Museum of Art

Wannan dorinar mai suna “William” an yi ta ne a Masar shekaru 4,000 da suka wuce. Yanzu haka yana gidan ajiye kayan fasaha na Meropolitan da ke New York na ƙasar Amurka.

Da akwai zakuna a duk faɗin Nijeriya. Amma a yanzu abin da ake da su ba su wuce 100 ba, kuma mazauninsu yana fuskantar barazana.

Copyright rizwansami789
Copyright rizwansami789

Ka shirya yin zane? Ka feƙe fensirinka, mu je zuwa! Ginshiƙan surorin abubuwa da dama su ne da’irori da surar ƙwai da kuma mazugi.

Copyright Polly Alakija

Ka tuna, da koyo akan iya!