KA AJIYE KOMAI KA YI ZANE
Giwa Ba ta Taɓa Mantuwa

Mu je ga zane kuma mu zana wasanmu na tunani.

Allah Ya yi wa giwa kaifin tunani domin tana iya tuna wuraren da za ta iya samun abinci da ruwa ta kuma iya tuna abokanta da abokan gabarta komai tsawon lokaci.

1. Ka yanke ‘yan guntayen takardu da siffar murabba’i.

2. Ka zana nau’i-nau’in dabbobi a kan murabba’in.

Mu fara wasan!

  1. Ka hautsina nau’o’in katin, ka baje su a kan tebur, suna kallon ƙasa.
  2. Ka riƙa juya su; biyu a lokaci guda. In an yi dacen iri guda wajen juyawar, sai abokin wasan ya riƙe su.
  3. Idan katin ba su zama iri guda ba, sai a mayar da su yadda suke: fuskar na kallon ƙasa.
  4. Hikimar ita ce don a tuna da wurin da kowane kati yake.
  5. Duk abokin wasan da yake da katin da suka dace da juna, to shi ne ya yi nasara!
Copyright Polly Alakija