KA AJIYE KOMAI KA YI ZANE
Yanzu sai mu Jojjona ɗige-ɗige
Ni Babba ne kuma Ina da Ƙarfi, Amma ina Buƙatar Kariya!
Inda yau muke da birane da mutane suke zaune a ciki zaman “Fuskance Ni In Fuskance Ka” a baya wajen dazuzzuka ne. Surƙuƙi da koguna wanda a da gidaje ne na dabbobi da tsuntsaye da kifaye kowane irin nau’i. Ta yaya za mu kare su idan suka kasance babu sauran inda za su zauna kuma?

Mai zanen bakin titi, SONNY yakan yi zanen fenti a kan dabbobin da suke fuskantar ƙarewa a birane. Wannan zanen bangon na dorinar ruwa nau’in Afirka ce a birnin Landon ta ƙasar Biritaniya.
Me kake gani za ka iya domin jawo hankalin mutane su riƙa bayar da kariya ga halittun da suke fuskantar barazanar ƙarewa?

Mai zanen bakin titi, ROA, da ke Bangkok, ƙasar Thailand. Giwaye su ma suna da ƙarfi amma suna buƙatar kariya!
Ka sauke ka kuma Aikata!
Copyright Polly Alakija
Ka jojjona ɗige-ɗige don ka yi naka hoton irin na ROA da SONNY.
Zanen fentin me za ka yi na wajen da kake da zama? Mene ne yake buƙatar kariya a muhallinka?