KA BA NI LABARINKA
Labari cikin surar ɗan lido: Nan take

Kana ina yanzu haka? Mene ne a kewayenka? Ka kwatanta abin da ka gani.

Me yake nan, a makon da ya gabata? A shekarar da ta wuce? Shekaru 50 da suka wuce? A shekaru ɗari biyu da suka wuce? Inda kake haka yake tun da can? Wa ya taɓa zama a nan kafin kai? Ko giwaye da kadoji sun taɓa zama kafin kai? Ko wurin da kurmi ne ko surƙuƙin daji?

Copyright Deposit Photos

A da can ruwa ne kwance a rairaiyin Sahara.

Copyright Painting by Heinrich Barth ,1858

Timbuktu, Mali 1858

Me zai kasance da nan a makwanni masu zuwa? A shekara mai zuwa? A shekaru 50 masu zuwa? A shekaru ɗari biyu masu zuwa? Waye ke nan zai kasance a nan ɗin? Kuma wannan wurin zai kasance mai tsabta da lafiya da kuma farin ciki? Ta yaya za KA iya mayar da wurin kyakkyawan wuri?

Copyright Tim Laman

Nan da muke da rijiyoyin mai da kuma birane, a da can surƙuƙin daji ne da hanyoyin ruwa.

Copyright blog.kugali.com

Shin haka za mu zauna a nan gaba?

1. A zana murabba’o’i a kan babbar takarda.

2. A rubuta shekara guda a kan kowane murabba’i. Ka koma can baya cikin tarihi da kuma nan gaba.

Story Board
Copyright Polly Alakija

3. Ka tsara ‘ya’yan lido guda biyu, za ka iya amfani da samfurin da ke nan.

4. A kan ɗan lido guda, sai ka zana dabbobi.

5. A kan ɗayan kuma sai ka zana lambobi.

Ka sauke ka kuma Aikata!

FCI Five Cowries Online My Story of Water 'Download and Do' Icon

6. Ka jefa ɗan lidon a kan kwalin, sai ka tsara labari a kan dabbar da ɗan lidon ya tsaya a kan ta. Lambar da ke kan ɗaya ɗan lidon shi zai nuna maka adadin dabbobin da ke cikin labarin naka.

MSOW_3_Story_Dice_2
Copyright Polly Alakija