KAI MA ZAKA IYA
Al'ajabi da Mamaki

Dabbobi sun samu ne tsawon milyoyin shekaru. Suna kare kansu ta hanyoyi mabambanta.
Sauya kama kan taimaka su ɓace wa mafarautansu.

Copyright https://listverse.com/
Copyright 2020 Allianz Australia Limited
Copyright Blend Space

Wannan nau’in kifi mai kamar ganye na teku da kifi mai dabbare-dabbaren launin ruwan lemo da kuma wannan hawainiyar sun saba ta yadda suke sajewa da muhallinsu.

Yanzu mu kirkiri wasu daga cikin mahaukatan dabbobinmu.

Kana bukatar:

Takardar kwali

Almakashi

Itatuwa

Fenti kaɗan in kana da shi

1. Idan kana da fentin, sai ka zana fentin wasu ‘yan alamomi a kan kwalin. Ka tuna yadda dabbare-dabbaren da ke jikin damisa da zanen jikin jakin dawa ko kuma ɓawon jikin kifi. Kai ma haka za ka zana waɗannan alamomin.

1 (1)

2. Ka yanke surorin daga kan kwalin.

2

3. Ka yanke ‘yan ramukan siffofin don su kasance a jejjere wuri guda.

IMG_3367 (1)
Copyright Polly Alakija

4. Ka fitar da ido da kunnuwa, sai jela da kaho. Sannan ka yi ka kara da sanya itatuwan don dabbar taka ta zama ta daban!

To yanzu ka sami mahaukaciyar dabbarka. Wane suna za ka ba ta?