KAI MA ZAKA IYA
Ka Zama Masassaki
Kafin masassaƙi ya yi wani babbar sassaƙa, galibi sukan fara da ƙanana da laka.
Ana kiran wannan da samfuri.

Samfurin damisa mai tafiya
Dylan Lewis 2012

Zomo Yana Zaune A Kan Katanga
Samfurin Guy Du Toit: samfurin zanen Zomo Cikin Annashuwa
Zanen dorinar ruwa mai suna William ta ƙasar Masar mai shekaru 4000 ita ta bayar da sha’awa ga masu zanen fasaha da dama.

“William”
Idan za ka sami laka a yankinku, kai ma za ka iya wannan! Ka fara da gwaji na wasu siffofi masu sauƙi. Kamar siffar ƙwallo da siffar ƙwai da kuma siffar kantu.