KAI MA ZAKA IYA
Kifin Jelly

Ana da nau’in kifin jelly a dukkan tekunan duniya fiye da shekaru 500 da suka gabata. Ana da nau’in kifin jelly ko kafin a san da dabbar dinosaurs. Kashi 95 cikin ɗari na jikin kifin jelly duk ruwa ne!

Copyright Uwe Nassal

Kifin jelly bai yaɗu sosai ba a tsawon shekaru milyoyi da suka gabata ba. Ba su da huhu ko ƙwaƙwalwa kuma ba su da jini. Su dai wasu halittu ne haka.

Copyright Project Manhattan

Kifin jelly suna harbi sosai. Yawan kifin jelly yana yaɗuwa sosai saboda sauyin yanayi.

Copyright GettyImages/Rost 9-D

Wannan samfurin kifin jelly ɗin yana da sauƙin sarrafawa. Abin da kawai kake buƙata shi ne kwalaben roba da kuma zare.

Copyright Polly Alakija

Idan ba mu kula da muhallinmu ba, za mu kasance tekunmu yana cike da kwalaben roba da kuma kifin jelly.