ME YAKE FARUWA A NAN?

Ko zaka iya tunanin yadda garuruwanmu da biranenmu suke?

Copyright John Eromosele
Copyright EnviroNews Nigeria 2020.

Gine-gine duk sun maye gurbin surƙuƙin bishiyoyi.

“Fuskance Ni In Fuskance Ka” shi ne sunan da muke kiran irin ginin nan da iyalai suke zaune kusa da kusa, a ɗakuna masu kallon juna. Da zarar yawan jama’a ya ƙaru, to haka ma biranen za su cakuɗe.

Copyright https://www.tv360nigeria.com/

A da Tsibirin Legas gonaki ne da kuma gidajen masunta da masu farautar kada. A da can kuma, mazaunin dorinar ruwa ne.

A lokacin da Nijeriya ta sami ‘yancin kai daga ‘yan mulkin mallaka na Biritaniya a 1960, adadin jama’ar ƙasar miliyan 45 ne. A yanzu, adadin jama’ar ƙasar miliyan 200 ne. Kila kuma a shekarar 2050, za a kai miliyan 400. A halin yanzu, kimanin mutane miliyan 63 a faɗin ƙasar ba sa samun tsaftataccen ruwan sha. Wannan ya nuna za a sami ƙarancin tsaftataccen ruwan sha da ƙarancin gonakin noma. Cututtuka kuma za su yaɗu cikin sauri.

Copyright ROA Mural

Hoton “Kada” daga New York, na mai zanen jikin bango PANGOLIN

Copyright EnviroNews Nigeria 2020.

A da, kogunan da suka kewaye Legas cike suke da kadoji da kifaye.

Copyright PJ KAPDostie
Copyright Jeff Amechi Agbodo, Onitsha

Ablade Glover mai zanen yanayi ne a kan tumbatsar birane, ɗan ƙasar Ghana. A inda muke da birane a yau, a shekarun baya dorinar ruwa ne a wurin.

Kogunanmu da hanyoyin ruwamnu da kurminmu ya kamata su kasance gida ne na nau’o’in dorinar ruwa da kadoji da kuma giwaye.

Copyright Harvey Barrison
Copyright AP Photo/Sakchi Lalit , Aug 13, 2017,Bangkok, Thailand.
Copyright San Diego Zoo Global

Nan ba da daɗewa ba wasu dabbobin za su ɓace. In hakan ta faru, mu kuma me zai faru da mu? Duk muna dogara da juna ne. Yana da kyau mu kiyaye dabbobin dajinmu daga farautarsu don hakan ma zai iya ƙarar da su. Yana da kyau mu kiyaye muhallinmu da mazaunin dabbobin daji don mu yi rayuwa cikin walwala da ƙoshin lafiya.

Polly Alakija