MU FARA SANYA LAUNI
Joseph Cartoon ɗan ƙasar Kenya ne.

Joseph yana son alamomi.
Kamar wani lokaci dabbobin da mutanen suna ɓuya ne a cikin hotunan, don da ƙyar ake iya ganin su.

Copyright Jospeh Cartoon
Copyright Jospeh Cartoon

Wani lokaci masu fasaha ba sa bai wa ayyukan nasu suna. Waɗannan zanen fentin guda biyu, “ba su da suna”. Shin wane suna za ka ba su?

Dabbobi da tsuntsaye da kifaye da dama sukan saje saboda haka ba a iya gane su. Wannan ɗaya ne daga cikin hanyoyin da suke kare kan su. Yanzu da ya kasance akwai mutane da yawa a duniya, babu isasshen wuri ga dabbobi saboda haka yana da kyau mu taimaka mu kare su.

Copyright Kate Mcalpine, University of Michigan
Copyright Tane Sinclair-Taylor,

Wasu daga cikin dabbobin da kifayen sukan iya canza warinsu ko ƙanshinsu don dai su kare kan su. Waɗannan kifayen sun yi kama da murjanin da ke kewayensu, saboda haka sukan iya canza wari ko ƙanshinsu daidai da na murjanin.

Ka sauke ka kuma Aikata!

FCI Five Cowries Online My Story of Water 'Download and Do' Icon
Copyright Polly Alakija

Ga wasu hotuna nan na Joseph ka sanya musu launi. Za ka iya ƙara naka alamomin. Za ka iya bai wa naka dabbobin da kifayen abin sauya kama?