MU FARA SANYA LAUNI
Na'urar kallon launin ƙwari
Christopher Marley masanin fasaha ne ɗan ƙasar Amurka. Ya zaga duniya yana neman kayan aiki da zai yi amfani da su.
Ya ƙirƙiri wasu kyawawan kayyaki da suke haska kyan dabbobi da ƙwari. Ya yi amfani da aikinsa domin shela a kan neman kariya ga muhalli na asali.

“Surar Launukan ƙwari”
Mukan dogara da duk nau’in ƙwari domin samun daidaito na yanayi. Kashi 40 cikin 100 na nau’o’in ƙwari suna fuskantar barazana. Me kuma dukkan dabbobi da tsuntsaye da kifaye za su ci?

“Aesthetica#1”
Akasarin ƙwari suna zuba ƙwayayensu a ruwa ne. Waɗannan ƙwayaye sukan kasance abincin wasu kifaye ne.

Tsutsar sauro.

ƙwaron mazari yana zuba ƙwai.
Ka sauke ka kuma Aikata!