MU FARA SANYA LAUNI
Shahararren Zanen Daji na Bango
A da can, inda a yanzu muke da birane cike da milyoyin jama’a, inda muke da surƙuƙin daji da hanyoyin ruwa da mazaunin milyoyin halittu ne.
Me kake zaton ya taɓa zama a inda gidanka yake yanzu?
Da akwai daji a wurin?
Da akwai kogi a wurin?


Wasu daga cikin masu zane na gefen titi sukan so kintacen wasu abubuwa da suke a wurin da gine-ginenmu suke.

Zanen gefen titi ya fara shahara ne daga muhimman tunani da kuma muhimman zane-zane.

Ya rage naka! Ka sauke waɗannan hotunan gine-ginen ka kuma zayyana su!
Ka sauke ka kuma Aikata!
Copyright Polly Alakija