MU JE GA YANKA
Kariyar 'Yansanda!
Giwa ce alamar ‘Yansandan Nijeriya. Me ya sa kake ganin hakan ta kasance?

Ka ga yadda ake alamta giwa a fasahar zanen duwatsu na gargajiya da sassaƙe-sassaƙe kuma a wasu lokutan a gine-gine. Giwaye suna alamta mulki da kuma ƙarfi.

Hauren giwar Bamileke daga ƙasar Kamaru.
A da Nijeriya tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suke da giwaye da yawa a duniya. Amma yanzu saboda yawan farauta da kuma sare dazuzzuka mazaunin giwayen, giwayen kaɗan ne suka saura.

Mai zanen bakin titi ROA, ya zana fentin jikin bango na dabbobin da suke fuskantar barazanar ɓacewa a bangaye da dama a duniya.
Ko kasan giwa tana shan ruwan da ya kai lita 200 a duk rana? Wannan ya kai kashi 100 na ruwan da kake sha!
Mafarauta kan kashe giwa domin su sami ganima.
Ana kashe dabbar fangolin saboda wasu suna da camfin cewa maganin da ake yi da ɓawon bayansa kan sa ƙarfi.


Dabbar fangolin a faɗin Afirka tana fuskantar barazana. ROA ya zana hoton fenti na fangolin a ƙasashen Afirka ta Kudu da kuma Gambiya.

Fangolin kan dunƙule kamar ƙwallo domin su kare kansu daga mafarautansu
Ka sauke ka kuma aikata!