MU JE GA YANKA!
Tarin tsuntsayen Penguin

LALLAI akwai Penguin a Afirka! Galibi nau’in halittar tsuntsun penguin suna zaune ne a yankin Antactica, amma a Afirka ma akwai irin nata nau’in.

Copyright Pinterest

Nau’in penguin na Afirka suna haɗuwa ne na har abada su kuma dawo wurin da suka haɗu a Afirka ta Kudu da ƙasar Namibia a kowace shekara domin su yi sheƙarsu.
Nau’in penguin na Afirka suna fuskantar barazana. A hankali ana gurɓata wurin zamansu saboda tsananin kamun kifi wanda hakan ya sanya babu isassun kifayen da za su ci su rayu.
Nau’in penguin na Afirka sukan yi nitso zurfin mita 120 a ƙasan ruwa domin su kamo kifi.

Copyright Pinterest

Yanzu bari mu tattara tsuntsun penguin.

Kana buƙatar takarda da fensir da almakashi da kuma ma’aunin tef.

Mu je zuwa!

Copyright Polly Alakija