SHIRI GA NUNI
A Ɗaure Ni Tare
Dabbobi sukan saba da kewayensu. Sun wanzu na tsawon milyoyin shekaru. Wuyan raƙumin dawa ya yi tsawo ne haka domin ya iya cin sabbin ganyaye da ke can saman bishiya.

Zanen jakin daji kuma yakan sa da ƙyar ake iya ganinsa cikin dogayen ciyayi a faɗin filin daji marasa bishiyoyi.

Kana buƙatar waɗannan domin haɗa ‘yartsanar nan:
1. Ninkakkun takardar kwali
2. Zare
3. Murafun kwalba
4. Bambaro
5. Ruwan gam da fenti (in akwai su).



