HADU DA MAWAKI
Donna Ogunaike

Donna lauya ce kuma mawakiya. Tana amfani da kalamai da kuma
wakoki don taimakon mutane wajen fadin labaransu.Mawakiya Donna tana rapping kuma tana raira waka.
Ku tuna cewa duk sanda kuke wanke hannuwanku dole kuyi amfani da sabulu
kuma zaku wanke hannun akalla na tsawon dakika ashirin.
Shin zaku iya hada waka wadda zatai tsawon sakan ashirin game da wanke hannuwa?
Ga wata waka da Donna tarubuta muku!

Ina godiya ga rana
Ina godiya domin kasa ta shuka
Ina godiya domin yanda suke wasa,
Kuma na dawo kamar ruwan damina.
Ina wasa a cikin wasan su,
Kuma na wanke tufafi na wani lokaci,
Dan feshin sabulu,
Da whoosh daga kumfan wanda yake kewaye yatsun hannuna,
Ta wannan hanyar,
Ina tsabta tare da wasa,
Domin kore wannan mummunar cutar.

Don haka ne kullum,
Ina gurje
Duk wani karamin abun tsoro.
Na fantsama kuma na fantsama,
Bana gaggawa,
Kuma na dauraye yatsu na tsap.

Ina raira waka ina aiki,
Domin ni ba sabon hannu bace,
Ina yinsa akalla sau shida a rana.
Yanzu ku murza hannuwanku tare,
Kuma ku raira waka idan sabulun na kumfa