HADU DA MAWAKI
Donna Ogunaike

Copyright Donna Ogunaike

Donna  lauya  ce  kuma   mawakiya. Tana amfani da kalamai da kuma
wakoki don taimakon mutane wajen fadin labaransu
.Mawakiya Donna tana rapping kuma tana raira waka.

Ku tuna cewa duk sanda kuke wanke hannuwanku dole kuyi amfani da sabulu
kuma zaku wanke hannun akalla na tsawon dakika ashirin.

Shin zaku iya hada waka wadda zatai tsawon sakan ashirin game da wanke hannuwa?

Ga wata waka da Donna tarubuta muku!

Copyright "Wash Day” Carlton Murrell Barbados

Ina godiya ga rana

Ina godiya domin kasa ta shuka

Ina godiya domin yanda suke wasa, 

Kuma na dawo kamar ruwan damina.

Ina wasa a cikin wasan su,  

Kuma na wanke tufafi na wani lokaci,  

Dan feshin sabulu,  

Da whoosh daga kumfan wanda yake kewaye yatsun hannuna,  

Ta wannan hanyar, 

Ina tsabta tare da wasa, 

Domin kore wannan mummunar cutar. 

Copyright Anthony Habis “Soap Suds and Bugs” mural. Children in Abeokuta, Nigeria

Don haka ne kullum,

Ina gurje  

Duk wani karamin abun tsoro. 

Na  fantsama  kuma  na   fantsama, 

Bana gaggawa,

Kuma na dauraye yatsu na tsap. 

Copyright UNICEF/UNI280305/Cote d'Ivoire

Ina raira waka ina aiki,

Domin ni ba sabon hannu bace, 

Ina yinsa akalla sau shida a rana.

Yanzu ku murza hannuwanku tare, 

Kuma ku raira waka idan sabulun na kumfa