NOTOCI DA BALTOCI
Me ya sa?

Me ya sa sabulu yake korar ƙwayoyin halitta?

Za ka buƙaci: 

Ruwa,

Busasshen barkono

Sabulun wanke-wanke

Fensiri da takarda

1. Ka zuba ruwa kaɗan a cikin kwanon.

2. Ka barbaɗa barkonon a cikin ruwan. Ka ga yadda yake yawo a kai?.Dalili shi ne wani sinadari na ruwan shi ya sa yake yawo a kai.

3. Ka tsoma yatsarka a cikin kwanon ruwan da barkonon ke ciki.Ko ka ji wani abu? Ka ɗauka cewa ɓurɓushin barkonon nan ƙwayoyin halitta ne.Ko ɓurɓushin barkonon nan sun maƙale maka a yatsa?

4. To yanzu ka tsoma yatsarka a cikin ruwan sabulun nan sannan ka mayar da yatsarka cikin ruwan.

5.  Me ya fara yanzu da ka sanya yatsarka mai sabulu cikin ruwan? Sabulun ya wanke ɓurɓushin barkonon! Soap breaks up the surface tension of water which is why it can chase away germs. Sabulu yana rugurguza wannan sinadari na ruwan don haka yake korar ƙwayoyin halitta.Wannan shi ne ya sa ake so kullum a riƙa wanke hannaye DA SABULU!

 Duk sanannun masana ilimin kimiyya da injiniyoyi sukan natsu tare da lura a dukkan wajen gwaje-gwajensu. Za ka iya zana hoton gwajin da ka yi na sabulu?

Copyright Tolu Ami-Williams and Sifon Ediomoo-Abasi

Ga wani babban zanen hannaye da sabulu da kuma qwayoyin cuta, yaya naka hoton zai kasance?