MEKE TAFYA NAN?

Wadanne abubuwa ne muke yi da hannuwan
Mu?

Copyright Adebanji Alade
Copyright Gerard Sekoto, South Africa.

Muna rubutu, da zane, da dafa abinci. Muna daukar abubuwa kuma mu ajiye su. Hannuwan Mu suna daukar jarirai kuma suna yin
Kitso.

Muna gaisawa da hannu don
maraba da juna, kuma Mu mika hannu don ban kwana

Copyright United Nation 1993.

Nelson Mandela ya gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a potugal a shekarar 1993.

Duba hannunka da kyau sosai. Shin da ga gaske suna da tsabta? Me kike dauke da shi a hannu ?  Shin zaku iya zana abubuwan da zaku Iya gani da kananan abubuwa wadanda baza Ku iya gani ba?

Copyright http://scientificanimations.com

Kwayoyin cuta kanana ne. Ba za ku iya gani su ba amma suna nan. Kwayoyin cuta suna a kan mabudan kofa, tebura, wurin, zama na bas, da jakunkuna suna jiran ka dauka su!

Duk lokacin da kayi atishawa ko tari zaka iya yada kwayar idan kana dashi yana iya yin tafiya mai nisa lokacin atishawa da tari har zuwa mita 7.

Copyright Kelly Sikkema