KIƊA TA AMFANI DA LAMBOBI

A tattaro tsoffin kwalaben gilashi.
A cike ruwa daidai gwargwado a kowace kwalba.
A zuba launi a ruwan.
Mu yi amfani da launin zoɓo a ruwan kwalaben kiɗa.

In aka ƙara yawan ruwan, launin zai ƙara haske.

Haka in aka ƙara yawan ruwan sautin kiɗan zai ci gaba da sauyawa in an buga.
A yi wa kwalaben kiɗan lambobi daga 0 zuwa 9.

Copyright Polly Alakija

Ko za ka iya fitar da wani sauti don yaranka su rausaya?