BARKA DA SHIGOWA SHAFIN INTANETI NA FIVE COWRIES

 Wai me muke yi ne?

Muna nan ne domin mu taikama ka inganta da kuma kyautata rayuwarka don gaba.

.Ga yadda abin yake ….

Waɗanne hikimomi kake buƙata domin cim ma burinka na zama uba ko malami ko manomi ko masanin lissafi ko masanin ilimin kimiyya ko injiniya ko mai shirya fina-finai ko mai kula da muhalli ko kuma marubuci?

 HAKAN YANA BUƘATAR HAƊIN GWUIWA DA SADARWA DA ƘIRƘIRA DA KUMA ƘWAƘƘWARAN TUNANI.

Sannan wane irin mutum kake fatar zama?

Kana son rungumar AL’ADARKA domin ka kasance mai kiyayewa da SADARWA da kuma HULƊA da AL’UMMARKA?

Ka ƙaddara kai maƙirƙirin fasaha ne kuma waɗannan kalmomi suna a matsayin sinadarai ne a fagenka.  Za ka sarrafa kalmomin, ka yi gwaji da su, ka koyi hikimomi ka kuma ƙirƙiri sabbin abubuwa domin kanka.

 Dukkan ayyukanmu za a iya yin su mutum shi kaɗai ko da iyalinsa. Abubuwan nishaɗi ne ga mutane masu mabambanta shekaru!

 Babu wata hanya ta nuna ƙwarewa ko kuma rashin ƙwarewa cikin ayyukanmu. Ka zaɓi duk abinda ka fi ƙauna, za ka iya zaɓar duk wani aiki a kowane lokaci a kuma ko’ina ne.

A shafin Five Cowries muna da dokoki biyar: A SHAƘATA!

YAYA IYA ƘIRƘIRARKA?

Ka kan yi haɗin gwuiwa ne ko mai son ganin ƙwaƙwaf ko mai biyayya ko mai zurfin tunani kuma mai juriya kake?  Masu koyo ko yaya shekarunsu suke za su iya tambaya a kan waɗannan tambayoyin?

 Za ka iya zana wili na kanka a matsayinka na ma’aikaci ko malami don ka tsara hanya mafi sauƙi domin yaran al’ummarka.

Ka sanya launi a da’irar ɓangaren da yake wakiltar yanayin fasaharka. Ɓangarori nawa za ka iya sanya wa launin? .Yanayin fasaharka ya haɓaka har zuwa wajen da’irar wilin.

KA LURA DA WANNAN!

 Me ya ja hankalinka?Me ka gani ko ka taɓa ko ka ji ko ka sansana ko kuma ka ɗanɗana da ya burge ka?

Ka lura, ko duba ko’inanka, ka riƙa tsara yadda za ka yi abubuwa. Za ka yi hakan ta hanyar zanawa ko rubutawa ko kuma duka biyun. Masu zanen fasaha da masana ilimin kimiyya da likitoci duk sukan riƙa lura da rubutu da yin tambayoyi, sannan sai su mayar da martani ta hanyar ƙirƙira.

Ka shirya?

 TO MU JE ZUWA