ME YAKE FARUWA A NAN?

Waɗanne irin kayan aiki kake buƙata?

Ka tattaro wasu abubuwa da yaranka za su yi abubuwa da su. Kwalaben roba da ƙyallaye da murfin kwalba da zare da maɓallai da tsoffin takardu da mujallu.

Ka adana waɗannan kayayyaki a tsaftataccen mazubi. Kowane abu da aka tanada a zuba shi a mazubinsa daban.

Ka bai wa yaranka tabarma, a shimfiɗa a ƙasa a matsayin “Tabarmar Koyo”.

Copyright Wasiu Quadri

Yaran za su yi amfani da ganyen ayaba wajen koyon saƙa tabarmar.

Ka ware wani lokaci a kullum na yin waɗannan ayyuka a kan “Tabarmar Koyon”.

Yaran su kasance a zaune yayin da suke yin yanke-yanke. Kar su riƙa nuna wani ko wani abu da almakashin.Idan ana riƙe da almakashi to bakin ya kasance a hannunka.

Abin sha’awa ne idan yaranka za su iya taimakawa a gida ko a gona ko kuma a kasuwa.Ka sa yaran su riƙa rubuta dukkan abubuwan da suke yi a gida, su kuma nuna jin ɗaɗinsu in an cike kowace taswira.

Ka riƙa tunatar da yaranka su riƙa wanke hannayensu kafin da kuma bayan kowane aiki.

Idan kana da wani safayar littafi to ka riƙa rubuta duk abin da iyali suke yi.. A kullum ka buƙaci wani daga cikin iyali su rubuta ko zana wani abu da ya faru a wannan ranar.Kowa ma daga cikin iyalin zai iya yin hakan!

Ka burge iyalinka wajen zana bishiyar li’irabin iyalinka.

Copyright Polly Alakija

Ka sauke tare da umurtar kowane mamba na iyalin ya zayyana kansa a wannan bishiyar iyalin.