MU TATTAUNA KAN KANO
Barka kadai Fatima! Sannu Fatima!
Fatima tana aiki ne da cibiyar Alliance Francaise ta Kano.

Fatima ta iya Hausa. Hausa shi ne harshen da aka fi magana da shi cikin Harsunan Afirka. Masu magana da shi sun kai mutum miliyan 150Akwai karuruwan harshen daban-daban a sassa da dama kamar a Ghana da Cadi da kuma Kamaru.
Kano shi ne birni na biyu a girma a Nijeriya. Tsohon birni ne kuma cibiyar kasuwanci tsakanin ƙasar Hausa da ƙasashen Larabawa ta yankin Sahara tun shekaru aru-aru.Kano ta zama masarauta a tsarin Musulunci a ƙarni na sha-biyu. A ƙarni na sha-tara Kano ta koma tsarin sarauta ƙarƙashin Daular Sakkwato. A da can birnin Kano gewaye yake da ganuwa. Za a iya ganin sauran waɗannan ganuwoyi a wurare daban-daban.

A cikin ƙwaryar birnin za a iya ganin wuraren rini na gargajiya.

A kowace shekara Sarkin Kano yakan shirya Hawan Daba da Sallar Azumi da kuma Sallar Layya.
