MU TATTAUNA KAN KWATANO

Barka kadai Stéphane! Ina kwana Stéphane!

Stéphane ya zo daga Kwatano ne. Shi Faransanci yake yi.

Copyright Poly Alakija

Kusan mutum miliyan 140 ne ke magana da Faransanci a ƙasashe 34 na Afirka.Harshen Faransanci ya zo Afirka ne ta hanyar mulkin mallaka.  Kwatano shi ne babban birni a Jamhuriyar Benin..Birnin yana shimfiɗe ne a tsakanin Tekun Atlantika da Tafkin Nokoué.

Copyright Gille C Photography

Mutanen wannan wuri suna cin kifi sosai.Abincin ƙasar Benin gauraye ne da na Afirka da irin na ƙasar Brazil da kuma Turai .Ana cin gasasshen kifi da miyar Moyo wadda ake yin ta da tumatir da barko ko kuma ka ci da Ago Glain, wadda miya ce da ake yi da dodon-koɗi da ƙaguwa sannan a haɗa da fufu.

Copyright IRD/C. Lévêque

Fadar gwamnatin Jamhuriyar Benin shi ne Porto Novo.

A Porto Novo akwai tsarin tsoffin gine-gine irin na ƙasar Brazil wanda ‘yan Afirkan da suka zauna a can suka kawo.

Copyright Musa Jibril

Garin ya fara ne a matsayin tungar masunta daga baya ya bunƙasa ya zama cibiyar kasuwanci..An yi cinikin bayi da manja da kuma auduga a wurin.

Copyright Happy Days Travel Blog