MU TATTAUNA KAN PORT HARCOUT

Barka kadai Onyinye! Ina kwana Onyinye!

Port Harcout shi ne babban birnin Jihar Rivers.

Copyright Polly Alakija

Jihar Rivers cike take da Koguna..Haka kuma akwai karuruwan harsuna da daban-daban. Ana yi wa jihar take da mai “harsuna 300”.. Bayan kasancewa Port Harcourt tungar masunta, ta kuma zama wata cibiya ta fitar da kwal zuwa ƙasashen waje lokacin mulkin mallaka, daga baya kuma ɗanyen mai.Wannan ya nuna cewa Port Harcourt ta bunƙasa zuwa babban birni.

Copyright Keith Arrowsmith

Har yanzu za a iya ganin tsoffin gine-gine na Turawan mulkin mallaka a Port Harcourt.

 

Abincin Bole da kifi haɗe-haɗe ne na gasasshiyar filanten ko gasasshiyar doya da kuma gasasshen kifi. Ana ci da haɗaɗɗiyar miyar manja.  Wannan shi ne kusan abincin da ake ci a Port Harcourt a matsayin na tafi-da-gidanka ko na yau-da-kullum dangane da yanayi ko lokaci.

Copyright Sharpsooters

Kuma kusan kowa yana sha’awar kwale-kwale a Jihar Rivers.A watan Mayu masu kwale-kwale sukan yi wata gasa ta Regatta a Port Harcourt.

Copyright Daily Times

Ana yi wa Jihar Rivers take da Jiha mai dodanni 1000.. A Port Harcourt a kowane watan Disamba akan yi bukin shekara-shekara na gargajiya. State.Kowa kan fito ya shiga wannan bukin al’adu na Jihar Rivers.

Copyright Finelib.com