MU TATTAUNA KAN LAGOS

Barka kadai Timiliyo! Ina kwana Timilayo!

Timilayo tana aiki ne da Alliance Francaise a Legas.

Copyright Polly Alakija

Timilayo ta iya Yarbanci. Mutane miliyan 55 ke magana da Yarbanci a Nijeriya da sauran sassa na duniya. Legas tana kusa da ikwuito wanda hakan ya sa a kullum take da zafi.. Legas tana da tashar teku mafi hada-hada a Afirka. Yarbawa suna zaune a nan tun ƙarni na sha-biyar., Legas ta zama tamkar gida ga al’ummomi na ƙabilu daban-daban na faɗin Nijeriya, da Afirka ta Yamma da kuma ‘yantattun bayi daga ƙasar Brazil da kuma Wuskindiyya.

Mutum miliyan 21 ke zaune a Legas. Sunan “Lago” yana nufin “tafki” a harshen Fotugalanci. Sunan “Lago” yana nufin “tafki” a harshen Fotugalanci. Legas ta zama babbar cibiyar cinikin bayi.Legas ta koma ƙarƙashin mulkin mallakar Biritaniyya a 1862.Ta zama babbar fadar gwamnatin Nijeriya har bayan mulkin kai a 1960. A 1991 ne fadar gwamnatin ta koma Abuja amma ta ci gaba da riƙe matsayinta na cibiyar kasuwanci ta Nijeriya.

Copyright Buzzfeed Nigeria

 Mutane da dama na sassan duniya sukan taka rawar kiɗa nau’in na Afirka na Fela Anikulapo Kuti wanda yake wasa a wurin da ake kira “The Shrine” a Legas.

Copyright Lemi Ghariokwu

Ga tambarin Jihar Legas.

Copyright Lagos State Government

Tambari yana ƙunshe da labari.

Farar Hular “Keremesi” ta kan Tambarin tana nuni da Sarakunan Gargajiya na Jihar Legas.

Copyright The Lagos Tempo News

A da can Legas mazaunin masunta da manoma barkono da kwakwa ne.Tana kewaye da ruwa da gaɓar teku ne, don haka an yi amfani da wuri wajen cinikayya.